in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da shugaban Masar Mohamed Morsy a Durban
2013-03-28 15:18:31 cri

Ran 27 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Masar Mohamed Morsy a birnin Durban na Afirka ta Kudu.

Yayin ganawar, Xi Jinping ya nuna cewa, kasar Sin ta mai da hankali sosai ga matsayin kasar Masar na babbar kasa mai tasowa ta al'ummar Larabawa, wadda ke nahiyar Afirka, mai kuma kunshe da al'ummar musulmi da dama, da irin tasirin da kasar ke da shi, Sin ta dauka zumuncin gargajiyar kasashen biyu da daraja sosai.

Haka zalika, Sin ta taya Masar murnar samun babban ci gaba a fagen sauyin siyasa, kuma ta lura sosai game da mawuyatan hali na 'dan lokaci da Masar din ke ciki a halin yanzu, Sin na burin ba da taimako yadda ya kamata ga kasar ta Masar.

A nasa jawabi, shugaba Mohammed Morsi cewa ya yi, kasar Masar tana matukar godiya ga fahimta, da goyon bayan da Sin ta nuna mata, kuma shugabannin Masar na son ci gaba da yin cudanya tare da takwarorin aikinsu na Sin, don gaggauta hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, da kuma karfafa hadin gwiwar kasashen biyu daga dukkan fannoni, bisa manyan tsare-tsare.

Kasar Masar na fatan daukar matakan da za su dace wajen kiyaye tsaron jama'ar Sin, wadanda ke son yin yawan shakatawa a yankunanta.

Yayin da suke tattaunawa kan batun Syria kuwa, shugaba Xi ya jadadda cewa, hanyar siyasa ita ce hanyar da ta fi dacewa wajen warware matsalar kasar Syria, Sin ta tsaya matsayinta na adalci wajen warware matsalar Syria a ko da yaushe. Bugu da kari, za ta nuna girmamawa, da goyon bayanta ga dukkan dabarun da za su samu karbuwa tsakanin bangarori daban daban da abin ya shafa wajen warware matsalar kasar.

Shugaba Morsi ya nuna cewa, kasar Masar na fatan za a kawo karshen rikicin kasar ta Syria cikin sauri, tare da mai da hankali sosai kan babbar gudumawar da Sin ta bayar kan batun. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China