Hua Chunying ta bayyana cewa, bayan da aka tabbatar da aukuwar lamari, gwamnatin Sin ta dora muhimmanci sosai game da batun, inda nan take, ma'aikatar kula da harkokin wajen Sin ta tura wani rukuni cikin gaggawa zuwa kasar ta Masar don nazartar wannan lamari. Hua Chunying ta ce, ofishin jakadancin Sin da ke Masar, da hukumar lura da harkokin wajen Sin da ke yankin Hongkong sun kafa tsarin ko-ta-kwana, don cudanya da sassan da abin ya shafa na gwamnatin yankin Hongkong, da taimaka ga ma'aikatan gwamnatin da kamfanin yawon shakatawa na Hongkong, da ma dangin wadanda suka mutu zuwa kasar ta Masar. Tuni dai ofishin jakadancin Sin da ke Masar, ya riga ya tura wasu wakilai zuwa wurin da lamarin ya auku.(Bako)