in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Masar
2014-06-06 15:31:31 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Mista Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Masar Nabil Fahmi, wanda ya zo kasar Sin domin halartar taron ministoci karo na 6 na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da kasashen Larabawa a ranar 5 ga wata a nan birnin Beijing.

Wang ya taya Masar murnar gudanar da babban zaben kasar yadda ya kamata, inda ya bayyana cewa, babban zaben ya zama wani muhimmin mataki a yunkurin siyasar Masar, yana fatan Masar za ta maido da zaman karko da bunkasuwa nan da nan, kuma za ta kara bayar da taimako da tasirinta wajen kiyaye zaman lafiya da zaman karko a shiyyar. Wang ya ci gaba da cewa, Sin ta nuna goyon baya ga kamfanoninta da su gudanar da hadin kai irin na moriyar juna dangane da bunkasuwar tattalin arziki a yankin mashingin ruwa na Suez, da hanyar dogo, da sabon makamashi da dai sauransu, wannan dai ya zama goyon baya da Sin ta nuna wa yunkurin wucin gadi na siyasar Masar.

A ganawarsu, Fahmi ya nuna godiya ga kasar Sin da ta nuna goyon baya ga yunkurin wucin gadi na siyasar Masar, ya ce, wasu abubuwan daga cikin shawarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar na raya tattalin arziki tsakanin yankunan da ke kan hanyar siliki ciki har da manyan ayyukan more rayuwar jama'a, da zirga-zirgar sararin sama da tauraron 'dan Adam, da sabon makamashi sun dace da shirin raya kasar ta Masar. Masar tana son yin amfani da wannan dama, don inganta hadin kai da kasar Sin a fannoni daban daban. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China