Da ta ke bayani ga manema labarai a nan birnin Beijing Madam Hua tace Sin na fatan za a tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a kasar nan bada dadewa ba.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, a safiyar yau, boma-boman da aka dasa cikin mota a dab da wani babban ofishin 'yan sanda a garin Mansoura dake arewacin kasar Masar sun tashi inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 14, yayin da wasu sama da dari suka jikkata.(Fatima)