Wang ya ce, matakin zai sassauta yanayin Syria, tare da samar da makoma mai kyau wajen daidaita batun makamai masu guba na Syria cikin lumana. Sin na fatan za a shigar da batun Syria a karkashin kulawar MDD cikin sauri domin sa kaimi a kai. Kamata ya yi kwamitin sulhu ya taka muhimmiyar rawa kan wannan batu. A sa'i daya, Sin na fatan kungiyar hana yaduwar makamai masu guba za ta gudanar da aikinta cikin adalci kuma bisa goyon bayan kasa da kasa.
Ban da haka, Wang ya jaddada cewa, matakan soja ba za su daidaita matsalar kasar Syria ba, kuma ya kamata a daidaita wannan matsala a siyasance, tare da sa kaimi ga yunkurin lalata makamai masu guba na Syria. Haka zalika mista Wang Yi ya yi kira da a tsagaita bude wuta a tsakanin bangarori masu gaba da juna a Syria, ta yadda za'a samar da yanayi mai kyau wajen soma lalata wadannan makamai da kuma shirya taron duniya na Geneva karo na biyu tun da wuri.(Fatima)