Kucherena ya ce, a ranar 16 ga wata, bisa goron gayyata da aka yi masa, ya yi shawarwari da Snowden a babban filin jirgin sama na Chelementievo, kuma sun tattauna batutuwan da ke shafar dokokin shari'a, daga bisani kuma, Snowden ya mika rokon neman mafaka ta wucin gadi ga ma'aikatan hukumar kula da shige da fice ta Rasha a hukunce, bayan haka, hukumar ta tabbatar da samun rokonsa, kuma ya ce, za a bukaci watanni uku domin dudduba wadannan takardu. Har ila yau, an ce, Idan aka amince da ba shi kariya ta wucin gadi, Snowden zai zama tamkar dan gudun hijira har na tsawon shekara guda, kuma idan yana son samun tsawaita lokacin, zai iya ci gaba da neman yin haka ba tare da kayyadadden lokaci ba.
A wannan rana kuma, sakataren kula da harkokin yada labaru na shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov ya bayyana cewa, gwamnatin Rasha ba ta samu takardun amince da sharadin da Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayar daga Snowden ba kan batun ba shi mafaka (Bako)