Bisa labarin da kafofin yada labaru na kasar Rasha suka samu, an ce, a ko wace rana, Amurka ta kan tattauna batun Snowden da kasar Rasha, kuma ta ja kunnen Rasha game da babbar illa da za a kawo wa dangantakar kasashen biyu, idan har Rasha ta baiwa Snowden mafaka.
Ban da wannan kuma, jakadan Amurka da ke kasar Rasha Michael kelhol ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, Amurka ba za ta bukaci Rasha ta mika Snowden ba, amma ta bukaci Rasha da ta kore shi.
Yanzu, Snowden yana jiran sakamakon hukunci da Rasha ta yanke masa game da rokonsa na neman mafaka.(Bako)