in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sarkin Kanon Najeriya zai nada Galadiman Kano a ranar Juma'a
2014-10-09 16:01:15 cri

Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, zai nada sabon Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi a ranar Juma'a mai zuwa, kamar yadda wata majiya daga masarautar ta bayyana.

Alhaji Mannir Sanusi, wanda shi ke rike da Sarautar Danmajen Kano, shi ya bayyana hakan a yayin wata ganawa da manema labarai da aka yi a Kano.

Ya ce nadin ya biyo bayan rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Tijjani Hashim ne, wanda ya rasu a ranar 28 ga watan da ya gabata. Kafin ba shi sarautar Galadiman Kano a ranar Lahadin da ta gabata, Abbas Sanusi shi ke rike da Sarautar Wamban Kano.

Haka kuma baya ga wannan sabon matsayin da ya bayar, mai martaba Sarkin ya baiwa dan marigayi Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero Sarautar Wamban Kano, inda a baya shi ke rike da Sarautar Tafidan Kano, yayin da kuma Alhaji Ahmad Ado Bayero, aka ba shi Sarautar Sarkin Dawakin Tsakar Gida.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China