Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Bauchi Haruna Mohammed ya tabbatar da cewa, mutane biyar sun kone kurmus yayin da aka garzaya da mutane 12 da suka ji raunuka daban-daban sanadiyyar fashewar zuwa cibiyar lafiya ta tarayya da ke garin na Azare.
Mohammed ya ce, koda ya ke ba a kowa ba game da wannan lamari amma tuni 'yan sanda suka killace wurin da lamarin ya faru tare da gudanar da bincike don gano musabbabin fashewar.
Wakilin Xinhua a jihar Bauchi ya bayyana cewa, ba a tabbatar ko kungiyar Boko Haram da ke haddasa babbar barazanar tsaro a Najeriya tun shekarar 2009 ce ta kaddamar da wannan hari ko a'a.
Sai dai masu sharhi na cewa, harin na garin Azare na iya mayar da hannun agogo baya kan tattaunawar yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyar Boko Haram. (Ibrahim)