A lokacin taron kwanaki uku da ake yi a shalkwatar rundunar tsaron dake Abuja Manjo Janar Chris Olukolade, kakakin rundunar wanda ya bayyana a cikin wata sanarwa ga manema labarai ya ce, ganawar wanda babban hafsan Sojin kasar na Kamaru zai halarta za'a yi shi ne karkashin jagorancin babban hafsan tsaron kasar Nigeriya Air Chief Marshal Alex Badeh tare da sauran tawagar soji bangarorin biyu.
Tattaunawar ta biyo bayan babban taron na kasa da kasa da ma na shiyya shiyya da aka yi domin inganta matakan tsaro, aka kuma samar da mafita wajen yaki da ta'addanci.
Wannan ganawar zai samar da sabon hanya da za'a bi don karfafa wanda aka riga aka samar na hadin gwiwwa tsakanin kasashen biyu dangane da yaki da ta'addanci. (Fatimah Jibri)