Wannan tasha da kamfanin ya gabatar a karo na farko za a rika kama ta a dukkan fadin kasar Najeriya, inda za ta rika gabatar da shirye-shiryen daban-daban ciki hadda fina-finai, kide-kide da sauransu, da zummar yada al'adun kabila mafi girma a kasar wato kabilar Hausa a kasar. Ban da haka kuma, wannan tasha ta zabi wasu jerin shirye-shirye na talibijin na Sinanci, wadanda aka fassara su, matakin da zai gabatarwa al'ummar Najeriya shirye-shirye masu kyau na kasar Sin, abin da zai baiwa jama'ar Najeriya wata dama mai kyau ta kallon shirye-shiryen kasar Sin, har ma su kara fahimtar al'adun kasar Sin da zurfafa mu'ammalar al'adu tsakanin kasashen biyu. (Amina)