in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya yi kiran da a samar da hadin kai a kasar
2014-10-05 16:17:33 cri

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sake nanata kudurin gwamnatin sa na tabbatar da hadin kai da zaman lafiyan kasar.

Shugaban wanda ya bayyana hakan a sakonsa na babbar sallah ga al'ummar kasar, ya kuma ce, gwamnatinsa za ta ba da fifiko ga kishin kasa maimakon wani buri na kashin kai ko yanki a lokacin da zai yanke shawarar tsayawa takara a shekara 2015 ko kuma a'a.

Shugaba Jonathan ya kuma bukaci 'yan siyasa da su himmatu wajen ganin daurewar mulkin demokuraddiya a kasar, bayan da hukumar zaben kasar ta Najeriya INEC ta bayar da wata sanarwar yiyuwar dage zabuka a kasar.

Sai dai shugaban ya ce, ya yarda kasar na fuskantar kalubale a wasu bangarori, duk da irin ci-gaba da ta samu a cikin shekaru hudu da suka gabata.

Ya kuma yi amfani da wannan dama wajen taya musulman kasar murnar babbar sallah tare da yi wa alhazai da ke aikin hajji a kasar Saudiya fatan alheri.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China