140924murtala0924.m4a
|
Gwamntin jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya ta bada tallafin kayayyakin da kudadensu ya kai kimanin Naira Miliyan 15 ga 'yan gudun-hijirar da suka samu mafaka a karamar hukumar Karasuwa don rage musu radadin halin rayuwar da suke ciki a sakamakon hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram da suka tilasa musu barin garuruwansu na asali a bangarorin jihohin Yobe, Borno da Adamawa.
Da yake mika kayayyakin tallafin ga hukumar kula da bada agajin gaggawa ta jihar Yobe (SERA), sakataren gwamnatin jihar Injiniya Baba Goni Machina ya ce wadannan kayayyakin agaji za'a bada su ne kawai ga al'ummomin da rikicin hare haren ta'addanci ya shafa, musamman wadanda suka yiwo hijira daga yankunan Kirenewa, Bama, Konduga, Baga, Maiduguri, Talala da Dambuwa a jihar Borno, da kuma wadanda suka fito daga garuruwan Buni Gari, Yadin Buni, Goniri, Bumsa , Bara da sauransu daga jihar Yobe.
Kayayyakin da gwamnatin ta bada tallafinsu sun hada da buhuna 200 na gero da buhuna 250 na shinkafa da buhuna 200 na masara da buhuna 350 na taliya da makamantansu.
Sauran kayayyakin da gwamnatin ta bada tallafinsu don rarraba su ga wadanda abin ya shafa sun hada da buhunan gishirin miya 310 da gidajen sauro 360 da kuma tabarmi 360.
Kayayyakin dai an danka su ne ga hannun babban sakataren hukumar bada tallafin gaggawa a jihar Yobe Alhaji Idi Jidanga wanda sakataren ya nemi jami'an hukumar da su mika wadannan kayayyaki ga wadanda wannan rikici ya shafa kai-tsaye ba tare da bata lokaci ba.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.