in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana tsaurara matakan yaki da Ebola a kan iyakokin Najeriya
2014-08-31 16:04:31 cri
Mahukunta a tarrayar Najeriya sun bayyana daukar karin matakan dakile yaduwar cutar Ebola a kan iyakokin kasar.

Ministan lafiyar kasar Khalliru Alhassan ya bayyana kafa sabon tsarin gudanar da sintiri na musamman, mai kunshe da tawagar ma'aikatan lafiya, tare da kwararru daga cibiyar dakile yaduwar cutuka ta kasar Amurka, da kuma wakilai daga tawagar likitocin Medicins San Frontiers.

Alhassan wanda ya bayyana hakan ya yin ganawar sa da 'yan jaridu a jihar Sokoto, ya kara da cewa ana fatan daukar wannan mataki, zai taimaka wajen yakin da ake yi da wannan annoba.

Game da yaduwar cutar ta Ebola a Nijeriya kuwa, ministan na lafiya ya ce kawo yanzu an tabbatar da harbuwar mutane 13, ciki hadda mutane 7 da tuni suka warke sarai, ya yin da kuma ake sanya ido kan wasu mutane 400, domin tantance matsayin su, bayan hasashen da ake yi cewa sun yi mu'amala da wadanda cutar ta kama a baya.

Cutar Ebola dai ta bulla ne a kasashen Guinea da Liberiya da Saliyo da Senegal da kuma Najeriya, tun a farkon wannan shekara da muke ciki, ya zuwa yanzu kuma ta hallaka mutane sama da 1,500 a kasashen 5 dake yammacin Afirka.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China