in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta tabbatar da mutuwar likitar nan wadda ta kamu da Ebola
2014-08-20 20:35:49 cri
Wata likita 'yar Najeriya da ta kamu da cutar Ebola lokacin da ta duba wani mai dauke da cutar ta mutu a jihar Ikko dake kudu maso yammacin kasar,kamar yadda mahukuntar kasar suka sanar.

Likitar da aka bayyana sunan ta Ameyo Stella Adadevoh kwararriyar likita ce da ta rasu a wurin da aka kebe ta a babban asibitin gwamnati dake Yaba a jihar Ikkon inji ministan kiwon lafiya Onyebuchi Chukwu cikin wata sanarwa.

Majiyar asibitin sun ce Dr Stella Adadevoh ta gamu da cutar ne lokacin da ta duba lafiyar Patrick Sawyer dan asalin kasar Liberiyan nan bayan da aka kebe ta tana jinya sai ta yi doguwar suma kafin mutuwar ta a jiya Talata. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China