in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kafa hukumar lura da harkokin samun bunkasuwa ta ECOWAS a kasar Togo
2014-11-20 11:10:47 cri

An kafa wata sabuwar hukuma da za ta rika kula da harkokin da suka shafi ci gaba karkashin kungiyar ECOWAS.

Hukumar mai suna PPDU an kafa ta ne cikin watan Oktombar da ya shude a birnin Lome hedkwatar kasar Togo. Za kuma ta kasance hanyar tantance ayyukan raya manyan ababen more rayuwar jama'a bisa muhimmancin kowannen su, bisa manufofin ECOWAS, da kasashe mambobin ta, da kuma hukumomi masu zaman kansu.

Ban da haka kuma, wannan hukuma za ta dauki nauyin zakulo hanyoyin da ake bukata wajen gudanar da wadannan ayyuka, da kara karfin tallafawa kasashe, da hukumomin gwamnatoci dake gudanar da ayyukan gina manyan ababen more rayuwa, tare da sa kaimi ga hadin gwiwa tsakanin kamfanonin kasashe, da masu zaman kansu ta fuskar tattara kudade. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China