in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana sa ran ECOWAS za ta cimma yarjejeniyar gina hanyar mota tsakanin Abidjan da Lagos
2014-02-25 15:14:23 cri

Wata majiya daga ofishin kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS, ta bayyana cewa, ECOWAS din za ta kira taron kolin ta a kasar Cote D'ivoire a watan Maris mai zuwa, inda ake sa ran za a daddale yarjejeniyar gina manyan hanyoyin mota tsakanin Abidjan da Lagos, aikin da zai ratsa kasashen da ke yammacin nahiyar Afrika.

Majiyar ta kuma ce kasashe mambobin kungiyar ta ECOWAS za su daddale yarjejeniyar tattara kudin aikin da bankin raya Afrika, tare da tabbatar da yawan kudin da ko wace kasa za ta biya don gane da wannan yarjejeniya.

An ce wannan hanya dake iya daukar motoci shida a lokaci guda, za ta dauki nauyin kusan kaso 75 bisa dari na sufurin kayayyaki tsakanin kasashen na yammacin Afrika. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China