in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ECOWAS za ta aiwatar da manufar harajin bai daya
2014-11-05 15:31:26 cri
Bisa labarin da kafofin watsa labarun kasar Senegal suka fitar a kwanakin baya, an ce, kungiyar ECOWAS za ta aiwatar da manufar biyan harajin bai daya kan ciniki tsakanin kasashen mambobinta, tun daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar badi.

Matakin dai zai kasance babban ci gaba ga yunkurin raya tattalin arziki bisa tsari na bai daya a yammacin Afirka, wanda kuma zai kyautata yanayin cinikin yankin, da kara samar da dama ga kasuwannin yankin mai mutane kimanin miliyan 300.

Wani mashawarci ga shugaban kasar Senegal ya bayyana cewa, aiwatar da wannan manufa muhimmin mataki ne na hade tattalin arzikin yammacin Afirka da na duniya, ta hanyar bunkasa ciniki da bada hidima cikin 'yanci, kana hakan zai sa kaimi ga canja yankin gudanar ciniki cikin 'yanci na kasashe masu amfani da harshen Turanci da Faransanci dake yammacin Afirka, zuwa kawancen kwastam na kasashen. Kaza lika matakin zai taimakawa wajen hana fasa kwaurin kayayyaki.

Ana dai yi hasashen cewa, bayan aiwatar da wannan manufa ta harajin bai daya, yawan harajin da za a buga ba zai wuce kashi 20 cikin dari ba, inda yawan haraji kan hatsi zai kai kashi 15 cikin dari, yayin da harajin da za a buga ga hatsin da ake shigarwa kasashen zai kai kashi 13 cikin dari. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China