Wadannan matakai biyu sun kasance mafi muhimmanci da aka cimma a kwanakin da suka gabata a yayin zaman taron musamman a birnin Dakar da ya maida hankali kan batutuwan tattalin arziki.
Cimma farashin harajin, da zai fara aiki a ranar daya ga watan Janairun shekarar 2015 na bude hanya kan kafa wata gamayyar harkokin kwastam dake kunshe da kasashen mambobi goma sha biyar na kungiyar ECOWAS.
Haka kuma tare da cimma wannan farashin, an samu wani dandalin kasuwanci mai karfi na yin gogayya, da zai iya kawowa kungiyar ECOWAS wani babban taimako a cikin harkokin musanyar kasuwancin duniya da kuma bunkasa kasuwanci tsakanin al'ummomi, in ji shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara, wanda ya kasance shugaban kungiyar ECOWAS a wannan karo.
Farashin nan wanda adadinsa aka yi hasashen cewa zai iya karuwa da kashi 35 cikin 100, za'a aiwatar da shi kan dukkan kayayyakin dake fitowa daga kasashen wajen shiyyar da zasu shiga a cikin yankunan kwastam na kungiyar ECOWAS. (Maman Ada)