Taron ya dora muhimmanci sosai kan wasu manyan batutuwa ciki hadda halin siyasa da ake ciki a kasashen Mali da Guinea Bissau, ta fuskar siyasa da tsaro, inda za a gudanar da manyan abubbuka.
Kasar Mali wadda ta fuskanci yakin basasa a taswon lokaci tun abkuwar juyin mulki a watan Maris na shekarar 2012, za ta yi zaben shugaban kasa a ran 28 ga wata. Rundunar taimakawa kasar Mali karkashin jagorancin kasashen Afrika musamman da kasshen kungiyar ECOWAS suka kafa ta cimma nasarar dakile masu tsatsauran ra'ayin Israma a arewacin kasar Mali, kuma an sake an canza rundunar zuwa Rundunar musamman ta MDD ta shimfida zaman lafiya a Mali a ran 1 ga wannan wata da muke ciki.
Akwai ma'ana sosai game da zaben shugaban kasar Guinea Bissau da za a yi. An kafa gwamnatin rikon kwarya, bisa shiga tsakanin da ECOWAS ta yi, bayan juyin mulkin soja da aka yi a ranar 12 ga watan Afrilu na shekarar 2012, kuma an yi shirin gudanar da babban zabe a ran 24 ga watan Nuwamba mai zuwa, inda hakan wata alama ce ta kawo karshen yamutsi da ake ciki tare da farfado da zaman oda da doka a kasar. (Amina)