Sanarwar ta nuna cewa, burin wannan tsari shi ne, daidaita abubuwa kamar yadda ya kamata a cikin kasashe mambobi na kungiyar ta fannin agaji, tsaron al'umma da ci gaba, dukkansu ta fannin yanayin taimako da jin kai.
Sanarwar ta nuna da cewa, kai agaji zai kasancewa ta fannin da ke da bukata, kamar ta bangaren rikici, abkuwar wani bila'in da ya faru ko kuma wanda aka jawo abkuwar shi, gudun hijira da kuma kariya ga 'yan gudun hijirar.
Taron zai yi kokarin tsara kudurori guda 7 da su ka kasance sa ido domin ganin an gudanar da tsarin a shara'ance, samar da shirin da ya dace da bada kariya idan lamura su ka taso a cikin gaggawa ta fannin bila'i,da tsara wasu hukumomi da za su kula da taimakawa ga lamuran agaji na gaggawa ta hanyar halartar wuraren da abubuwa suka abku, da karfafama kungiyoyin sa kai wajen gudanar da hidamar agaji, da sa ido ga kasashe mambobin kungiyar da su gudanar da ayyuka kamar yadda dokokin kasa da kasa game da kare fararen hula su ka amince da a yi. Bugu da kari kudurorin sun hada da dokar daukar matakan rage wahala kan fararen hula a lokacin tashin hankali, da bunkasa matakai na musamman wajen kare al'umma mai rauni musamman mata da yara a lokacin ceto, da kuma kayyade amfani da kafofin sadarwa ta hanyar yin amfani da kungiyoyin agaji a matsayin wadanda su ka dace su taimaka wajen magance lamuran da su ka faru ga al'umma. (Abdou Halilou)