Hakazalika sanarwar ta cigaba da cewa mista Coulibaly zai kuma halarci ayyukan zaman taro na 67 na MDD a birnin New York da za'a bude a ranar Talata mai zuwa.
Kafin ya isa birnin New-York, minista Coulibaly, bayan birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire, zai kuma isa birnin Paris domin habaka dangantakar dake tsakanin kasarsa da kasar Faransa sannan kuma ya wuce zuwa birnin Bruxelles, cibiyar tarayyar Turai in ji wannan sanarwa. (Maman Ada)