in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan majalissar dokokin kungiyar tarayyar tattalin arzikin yammacin Afrika ta yi kira da a karfafa yaki da ta'adanci a yankin
2013-01-22 20:55:24 cri
'Yan majalissar dokoki daga kasashen kungiyar tarayyar tattalin arzikin yammacin Afrika ECOWAS a ranar talata 22 ga wata suka yi kira ga sauran kasashen dake cikin wannan kungiya dasu nuna kokarin su da kuma goyon bayan wajen yakan ta'addanci a cikin wannan yanki da ma duniya baki daya.

Kakakin wannan majalissar Ike Ekweremadu daga Nijeriya wanda ya sheda ma manema labarai hakan a Abuja ya ce ana bukatar a maida hankali sosai wajen yaki da kuma rage ta'addanci zuwa wani matsayi mafi kankanta a yanki,sannan kuma ya yi Allah wadai da hare haren da ake kaiwa wassu kasashen mambobin wannan kungiya da suka hada da Nijeriya,Mali da kuma Niger.

Kakakin majalissar na yammacin Afrika ya kuma yaba da kokarin shugabannin kasashen wannan yankin na tallafawa gwamnatin kasar murkushe dakaru daga arewacin kasar da suke da alaka da al'Qaida.

Yace "mun yaba da kokarin shugaban wannan kungiyar ta ECOWAS saboda himmar sa na ganin an samar da taimakon shiga tsakani musamman a kan dukkanin kokarin da sauran shugabannin yammacin kasashen Afrika don ganin sun samu amincewar MDD na daukar wannan mataki mai lamba 2085." (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China