in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kungiyar ECOWAS sun amince da tura sojoji zuwa kasar Mali
2012-11-12 21:06:22 cri
A jiya Lahadi 11 ga wata,cibiyar kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afrika ECOWAS dake Abuja birnin tarayyar Nigeriya ta tsaida shawarar tura sojojinta zuwa kasar Mali domin fatattakar dakarun 'yan tawaye da suka rike arewacin kasar a yanzu haka domin a dawo da dauwamammen zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali.

A cikin wata sanarwa daga cibiyar a yau Litinin 12 ga wata, an ce kungiyar ta yanke shawarar ne sakamakon wani taro na musamman da ta kira na shugabannin kasashen kungiyar domin bukatar kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ya amince da tsarin matakin da ya kamata a dauka, wanda shugabannin suka tattauna a kai tare da dabarun da ya kamata a bullo da su domin aikawa da su zuwa ga kwamitin sulhu na MDD.

Kungiyar ta ECOWAS wanda ta bukaci kwamitin sulhu na MDD da ta yi nazarin tsarin da zummar bada umurnin aikawa da sojoji zuwa Mali kamar yadda sashi na 7 na kundin tsarin majalisar ta tsara, har ila yau ta yi bayanin cewa, wannan bukata dole ne a amince da ita kafin ranar 15 ga wata kamar yadda tsarin majalisar mai lamba 2071 ya shimfida.

Sanarwar kungiyar sai dai kuma ta yaba ma kokarin kasar ta Mali na amfani da nata sojojin tare da shawarwari domin samun maslaha a cikin halin da take ciki, tare da bayanin cewa, ya zama wajibi ga ECOWAS ta yi amfani da matsayin shugabancinta wajen aikawa da sojoji. A cewar sanarwar, wannan mataki zai rage nauyin da ke kan wuyan kasar ta Mali wajen kokarin kawo zaman lafiya da kuma rage mata nauyi idan ta hada hannu tare da AU da ECOWAS da kuma MDD.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China