in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ECOWAS ta mika sakon taya murna ga kungiyar kwallon kafa Super Eagles ta Najeriya
2013-02-13 16:18:42 cri
Shugaban kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma ECOWAS Kadre Ouedraogo ya taya kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles murna dangane da nasara da ta cimma na zama zakaran gasar kwallon kafa cin kofin Afirka jiko na 29 da aka yi a Afirka ta kudu.

A cikin wata sanarwa ranar Litinin a Abuja, Ouedraogo yace wannan nasara da kungiyar ta Super Eagles ta cimma sakamako ne na hazaka da kwarewa na kungiyoyin dake yankin.

Shugaban kungiyar ya kuma yabi daukacin kungiyoyin kwallon kafa guda takwas na kasashen yankin Afirka ta yamma dangane da cimma nasarar kasancewa a matsayi guda 4 mafi daraja, a gasar da aka fafata tsakanin kasashe 16.

Ya ce kungiyoyin ko shakka babu sun nuna bajinta a fuskar da'a da iya wasa.

Ya ci gaba da cewa kungiyar da mutanen yankin baki daya suna masu alfahari da wannan nasara da kuma iya wasa da kungiyoyin kwallon kafa na yankin ECOWAS suka nuna, musamman ma kungiyoyi bakwai da suka samu buga wasan dab da na kusa da na karshe.

Ouedraogo ya kuma kara da cewa rawar gani da kungiyoyin kasashen yankin ECOWAS suka yi a wasan na cin kofin Afirka AFCON na shekarar 2013 ya kara nuna cewa su ne ke kan gaba a fagen kwallo a nahiyar.

Ya ce yadda suka buga wasannin ya nuna irin hazaka da matasan ke da shi wanda kuma yankin ke cin amfaninsa don bunkasar yankin baki daya. (Lami Ali Mohammed)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China