in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ECOWAS ta shirya taron gaggawa kan rikicin Mali
2013-01-20 17:18:15 cri
Ranar Asabar 19 ga wata, a birnin Abidjan na kasar Kodivwa, kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka ECOWAS, ta gudanar da wani taron shugabannin kasashen yankin na gaggawa, inda aka tattauna yadda za a hanzarta daukar matakan soja, domin tinkarar rikicin da ke wanzuwa a arewacin kasar Mali.

Alassane Ouattara, shugaban kasar Kodivwa, kuma shugaban zartaswa na kungiyar ta ECOWAS, ya yi jawabi a yayin taron, inda ya yi kira ga babban sakataren MDD, da kwamitin sulhun majalissar da su zartas da shirin ba da taimakon kudi da kayayyakin guzuri, da kafa asusun musamman domin goyon bayan matakan soja da ake dauka a Mali, cikin sauri ba kuma da wani bata lokaci ba. Bugu da kari, Shugaba Ouattara ya yi kira ga ragowar kasashen duniya, da suma su shiga shirin daukar matakan soja, dake gudana,domin maido da arewacin kasar ta Mali hannun gwamnatin kasar, su kuma hada kai da kasar Faransa da kuma ragowar kasashen Afirka.

Tuni mista Ouattara ya sa hannu kan wata sanarwa, inda ya baiwa kasashe mambobin kungiyar ECOWAS iznin tura sojojin su zuwa Mali cikin gaggawa, a kokarin mara wa sojojin gwamnatin Mali baya wajen yaki da dakarun da ke arewacin kasar.

Yayin dai da shugaba Goodluck Jonathan na Nijeriya ke halartar wannan taron na ECOWAS a Abidjan, aka kai harin bom kan wani rukuni na sojojin Nijeriyar, dake shirin tashi zuwa Mali a jihar Kogi dake tsakiyar Arewacin kasar, inda nan take sojoji 2 suka rasa rayukan su, yayin da wasu 5 suka jikkata.

Har wa yau kuma, shafin yanar gizo na ma'aikatar tsaron kasar Faransa, ya watsa wani labari a ran 19 ga wata, dake nuna cewa, daga daren ranar 18 zuwa daren ranar 19 ga wata, jiragen saman yaki na Faransa fiye da goma, sun ci gaba da kai hare-hare kan dakaru masu tsattsauran ra'ayin Islama da ke garin Diabaly. Ya zuwa ranar 19 ga wata, Faransa ta jibge sojojin ta dubu 2 a Mali, wadanda suke hadin gwiwa da takwarorinsu na Mali wajen tsaron yankin kogin Nijer, a kokarin hana dakarun masu tsattsauran ra'ayoyin kai wa birnin Bamako, hedkwatar kasar hari. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China