in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban ECOWAS ya yi kira da a tallafawa kungiyar a kokarinta na dakile ta'addanci
2013-10-26 17:00:23 cri
Shugaban karba-karba na kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka (ECOWAS), kuma shugaban kasar Kwadebuwa, Alassane Ouattara, ya yi kira ga gamayyar kasashen duniya, da su kara baiwa kungiyar tallafi, a kokarinta na dakile ayyukan ta'addanci a yankin Sahel dake yammacin Afirka.

Shugaba Ouattara wanda ya yi wannan kira a ranar 25 ga watan nan, yayin bikin bude taron shugabannin kungiyar ta ECOWAS na musamman da ya gudana a birnin Dakar, fadar mulkin kasar Senegal, inda ya kara da bayyana bukatar baiwa ECOWAS karin tallafin fatattakar 'yan ta'adda a yankin na Sahel, gami da kau da lamuran da ka iya haddasa rashin tsaro. Har wa yau kuma, shugaban kasar ta Kwadebuwa ya bayyana fatansa, na ganin gamayyar kasa da kasa sun karfafa matakan yakar gungun masu aikata laifuka a wannan yanki.

Yankin Sahel wanda ke kudu da hamadar Sahara, dake da fadin kimanin kilomita 320 zuwa 480, ya kuma ratsa kasashen Senegal, da Mauritaniya, da Mali, da Burkina Faso, da Nijar, da dai sauransu, na shan fama da ayyukan ta'addanci, da rikice-rikice, da kungiyoyi masu aikata laifuka daban daban ke gudanarwa a 'yan shekarun nan.

Cikin jawabinsa, mista Ouattara ya yi kira ga kasashe mambobin kungiyar ta ECOWAS, da su yi hadin gwiwa da kasar Mali, don kau da barazanar ta'addanci da kasar ke fuskanta. A cewar sa, mawuyacin halin da kasar Mali ke ciki, ya shaida muhimmancin dake akwai, ga hadin kan kasashen kungiyar ta ECOWAS, wajen fuskantar wadannan kalubaloli. Daga nan sai ya yi alkawari a madadin ECOWAS, cewa za a tallafawa aikin sake gina kasar ta Mali. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China