in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi alkawarin ci gaba da baiwa Afirka tallafin yaki da cutar Ebola
2014-10-31 20:31:01 cri
A yau Jumma'a ne kasar Sin ta yi alkawarin ci gaba da aika tallafi zuwa kasashen nan na Afirka da ke fama da barkewar cutar Ebola, bayan da a makon da ya gabata ta bayyana cewa, tana shirin aike wa da kashi na hudu na tallafin zuwa wadannan kasashe.

Darektan sashen kula da harkokin Afirka na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Songtian wanda ya sanar da hakan ya ce, kasar Sin ba za ta daina tallafawa kasashen na yammacin Afirka ba muddin ba a kawar da wannan cuta ba.

Ya zuwa yanzu kasar Sin ta tallafawa kasashen yammacin Afirka da ke fama da wannan cuta da agajin da ya kai dala miliyan 122.

A makon da ya gabata shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayar da sanarwar baiwa kasashen Liberia,Saliyo da Guinea da ke fama da cutar Ebola tallafin da ya kai dala miliyan 82.

Tun lokacin da cutar ta barke a watan Fabrairu, kasar Sin ta baiwa kasashen da ke fama da cutar ta Ebola a yammacin Afirka tallafi kashi 3, wadanda suka hada da watannin Afrilu, Agusta da kuma Satumba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China