Cikin sanarwar, kwamitin ya ce, akwai rahotanni dake nuna cewa an kai hare-haren boma-bomai a wani sansanin 'yan gudun hijira a lardin Iblid na kasar a ranar 29 ga watan Oktoba, hare-haren da suka haddasa mutuwa da jikkatar mutane da dama, ciki hadda da wasu yara kanana.
Dangane da hakan, kwamitin ya nuna matukar bacin ransa, yana mai jaddada matukar bukatar mutunta dokar jin kai ta kasa da kasa, musamman ma batun bambancin dake tsakanin fararen hula da sojoji a yayin da aka kai hare-hare.
Sanarwar ta bayyana fatan kwamitin game da kauracewa kaiwa fararen hula hare-hare da ma duk wasu lamura masu alaka da hakan. (Maryam)