Kasar Sin a yau Talata 15 ta sanar da jin dadinta game da shawarar da kwamitin tsaron MDD ta zartas game da warware rikicin kasar Sham tare da yin kira ga dukkan bangarorin da hakan ya shafa da su aiwatar da wannan kuduri ta hanyar daukan matakai masu amfani.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei da yake mai da martani game da kudurin kwamitin mai lamba 2165 da aka zartas ranar Litinin lokacin taron manema labarai na wannan rana a nan birnin Beijing ya ce, kasar tana dora muhimmanci sosai na son ganin an sassauta halin jin kai da al'ummar kasar Sham ke fuskanta, don haka tana son ganin an mai da himma na ganin an samu maslaha, shi ya sa ita ma Sin take son ba da nata gudumuwa. (Fatimah)