Sanarwar ta bayyana cewa, wannan wani babban ci gaba ne a aikin lalata makamai masu guba na kasar Syria. Ban Ki-moon ya nuna yabo ga kokarin da gwamnatin kasar Syria ta yi kan wannan lamari, kana ya nuna yabo ga kasashe membobin MDD na nuna goyon baya ga aikin da tawagar wakilan kungiyar haramta makamai masu guba da MDD suka yi. Ban da wannan kuma, Ban Ki-moon ya kalubalanci kasar Syria da ta tabbatar da cewa an lalata dukkan makamanta masu guba.
Kasashe da dama ne suka shiga aikin lalata makamai masu guba na kasar Syria, a ciki, kasashen Denmark da Norway suka dauki nauyin jigilar makaman ta jiragen ruwa, sa'an nan kasar Amurka ta lalata su a kan teku, Sin da Rasha kuwa sun tura jiragen ruwan soja don ba da kariya.(Zainab)