Mataimakin faraministan Syria, Walid al-Mouallem ya zargi gwamnatin kasar Amurka a ranar Litinin da amfani da ma'auni biyu wajen yaki da ta'addanci.
A cikin jawabin da ya gabatar a babban taron MDD, mista al-Mouallem, kuma ministan harkokin wajen Syria, ya yi allawadai da abun da yake kira siyasar Amurka ta ma'auni biyu, dake nuna bukatar yaki da ta'addanci tare kuma da cigaba da samar da kudi da makamai ga kungiyoyin da Amurka take kira masu sassaucin ra'ayi.
Wannan ba ya da wata ma'ana, illa kara karfafa rikici da ta'addanci, kara tura mutane cikin tashin hankali, da kuma kara tsawon rikicin Syria ta hanyar lalata gishiken cimma mafita ta siyasa. Wannan mataki na kara kafa wani yanayi mai kyau ga kungiyoyin ta'addanci dake aikata munanan keta hakkin dan adam a cikin kasar Syria, in ji mista al-Mouallem.
Haka kuma ya bayyana cewa, kasarsa ta shiga yaki da kasar Musulunci ta Iraki da Levant (ISIS), kungiyar ta'addanci mafi illa ga duniya, tare da yin kira ga gamayyar kasa da kasa da ta tallafa wa wannan yaki domin bazaranar ba ta tsaya kawai ga Iraki da Syria ba.
Mataimakin faraministan Syria ya tunatar da cewa, ISIS ta samu taimakon kudi da makamai kafin ta shiga mamaye wasu yankunan Syria da Iraki.
Ya kamata mu matsa lamba kan kasashen dake samar da tallafi ga wadannan kungiyoyin ta'addanci, domin an san wadannan kasashe sosai, in ji mista al-Mouallem. (Maman Ada)