A ranar Litinin din nan 14 ga wata, kasar Sin ta bukaci da a aiwatar da shirin nan na zirga-zirga a kan iyaka da kwamitin tsaro na MDD ta amince da shi domin ba da dama a isar da kayayyakin agaji ga mabukata a kasar Sham.
Liu Jieyi, wakilin din din din a majalissar ya yi wannan kira a zaman kwamitin wanda ya amince da wannan bukata mai lamba 2165 da zummar kara kafofin isar da kayayyakin agaji ga fararen hula da ke zaune a wurare mai wuyan shiga ta hanyar bi ta kan iyakoki da inda aka rika aka kebe a matsayin wajen tashin hankali.
Mr. Liu ya yi nuni da cewa, amincewar mambobin kwamitin gaba daya za ta saka wannan kuduri zama abu mafi muhimmanci ga kwamitin da sauran kungiyoyin kasashen duniya a game da agajin da ake baiwa Sham.
Wajen tafiyar da ayyukan agaji, MDD da sauran hukumomin kare hakkin bil adama ya kamata su yi aiki bisa ga tsarin kwamitin, su mutunta mulkin kan kasar Sham, 'yancin ta, hadin kai da ikon mallakar iyakokinta, haka kuma a bi tsarin MDD a kan ba da agajin gaggawa, a kuma yi kokarin samun fahimta, goyon baya da hadin kai daga kasar. In ji Mr. Liu.
Wakilin na kasar Sin ya jaddada goyon bayan kasarsa a kokarin sauran hukumomin duniya musamman MDD suke yi wajen sassauta halin da ake ciki a kasar ta Sham.
Ya kuma tabbatar da cewa, hanyar siyasa ce kadai wadda za'a iya bi wajen magance halin da ake ciki, don haka ya yi kira ga kasashen duniya da su tsaya kan ganin an warware wannan matsala a siyasance, a kuma cigaba da hadin kai da tattaunawa. (Fatimah)