Shugaban kasar Syria Bachar al-Assad ya rantse a ranar Laraba da cigaba da yaki da ta'addanci, tare da bayyana cewa, kasashen shiyyar da kasashen yammacin duniya dake taimakawa mayakan kungiyoyin ta'addanci a kasarsa za su dandana kudurinsu da yin da na sani.
Ba za mu tsaya ba wajen yaki da ta'addanci, kuma za mu yi shi a ko'ina har sai mun tabbatar da zaman lafiya a ko'ina a kasar Syria, in ji Al-Assad a ranar Laraba a cikin jawabinsa na kama aikinsa a matsayin shigaban kasa a cikin wa'adi na uku na shekaru bakwai.
Gwamnatin Syria ta bayyana cewa, tun tsawon lokaci ne take yaki da 'yan ta'addan dake samun tallafi daga kasashen ketare masu adawa da hukumomin kasar tun farkon yakin basasa a wannan kasa. (Maman Ada)