Bugu da kari, bayan da ta gabatar wa kwamitin sulhu na MDD yadda aikin ke gudana, Ms.Kaag ta bayyana wa kafofin watsa labarai cewa, ya zuwa yanzu an lalata kashi 96 bisa dari na sinadaran makamai masu guba da gwamantin kasar Syria ta gabatar, sa'an nan ya zuwa karshen watan nan da ake ciki na Satumba, tawagar hadin gwiwa ta kungiyar OPCW da MDD za ta kawo karshen wannan aiki.
Daga nan sai Ms.Kaag ta ce, a farkon watan Oktoba kungiyar ta OPCW za ta fara aikin halata sauran kayayyakin makamai masu guba dake wurare 12 a kasar Syria. (Maryam)