in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Obama ya amince da amfani da jiragen sama domin sa ido kan Syria
2014-08-27 14:07:07 cri

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya amince da amfani da jiragen sama domin sa ido a kan kasar Syria, shugaban ya yi haka ne a daidai lokacin da ake ta muhawara a kan yiwuwar Amurka ta kai hari a kan wuraren da kungiyar Islama ta ISIS ta mamaye a kasar Syria, wacce yaki ya daidaita.

Hukumar tsaro ta Pentagon ta ce, jiragen da za su sa ido a kasar ta Syria, za su yi amafani da jiragen, kila ma har da jirage na leken asiri, kuma jiragen za su maida hankali wajen sa ido a kan iyakar tsakanin Syria da Iraq, duk da yake cewar, kungiyar Islama ta mai da wurin kamar ba wata kan iyaka, saboda yadda take ta kutsawa da hare-haren da take kaiwa.

Jaridar New York Times ta ruwaito cewar, wani babban jami'in gwamnatin Amurka, ya ce, Obama shi ne ya bayar da iznin gudanar da aikin sa idon a kan kungiyar Islamar a karshen mako, kuma yanzu haka hukumar tsaro ta Pentagon tana duba yiwuwar kai hari a kan iyakar Syria a maimakon kai harin lungunan kasar ta Syria.

A halin da ake ciki dai fadar White House na duba yiwuwar yadda kai harin da za'a yi a kan kungiyar Islamar ba zai taimakawa ba gwamnatin shugaban Syria Bashar al-Assad ba, domin Obama ya sha kiran da a sauke Bashar al-Assad daga mulki. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China