Ana ci gaba da samu gagarumin ci-gaba a aikin lalata sinadarai masu guba da ka fitar daga kasar Syria, in ji shugaban karba-karba na kwamitin tsaron MDD, kuma wakilin din-din-din na kasar Ingila a MDD Mark Lyall Grant a jiya Talata ranar 5 ga wata.
Mark Lyall Grant wanda ya bayyana hakan jim kadan bayan ganawar sirri da ya yi da 'yan kwamitin tsaron MDD 15 ta allon talabijin, ya kara da cewa, jami'an aikin lalata sinadaran na kasar Amurka, sun kammala kusan kaso 60 bisa dari na aikin da suke gudanarwa, kuma da zarar sun kammala za a tura birbishin sinadaran zuwa kasar Jamus, domin kammala matakin karshe na aikin.
Kaza lika ana sa ran su ma jami'an kasar Birtaniya za su kammala nasu aikin nan gaba cikin wannan mako.
A wani ci-gaban kuma, an sanar da wakilan kwamitin tsaron MDD game da wani taro da ya gudana a birnin Beirut a ranar Talata, taron da ya maida hankali ga nazartar hanyoyin lalata wasu nau'o'i 12 na sinadaran masu hadari da suka rage, aikin da za a kwashe kusan watanni 6 ana gudanar da shi.(Saminu Alhassan)