Hukumar tsara shirin abinci ta duniya wato WFP ta nuna godiya ga taimakon da Sin ta bayar wajen yaki da cutar Ebola,inda ta ce,abu mai muhimmanci wajen tabbatar da aikin yaki da Ebola shi ne samun isashen kudi don tallafawa jama'ar dake fama da cutar Ebola.
Wakilin hukumar Brett Rierson ya bayyana a gun taron manema labaru a wannan rana a nan birnin Beijing cewa, gwamnatin kasar Sin ta baiwa hukumar tallafin kudi dala miliyan 6 a farkon wannan wata da muke ciki, don tallafawa aikin da hukumar ke yi a kasashen Guinea, Laberiya da Saliyo, wanda zai taimakawa mutane fiye da miliyan 1.3 dake fama da cutar. (Amina)