in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Sin ta baiwa WHO kudin kyauta don yaki da cutar Ebola
2014-10-23 20:20:31 cri
Bisa labarin da aka samu, an ce, a madadin gwamnatin kasar Sin, mai ba da taimako ga ministan harkokin kudin na kasar Sin Zhang Xiangchen ya kulla wata yarjejeniyar hadin gwiwa tare da wakilin musamman na hukumar lafiya ta duniya WHO dake kasar Sin Dr. Bernhard Schwartlander a ran 21 ga wata, dangane da samar wa hukumar kudin kyauta musamman na dallar Amurka miliyan 2 don fuskantar cutar Ebola.

Za a yi amfani da kudaden ne a kasashen uku da suka hada da Saliyo, Liberia da kuma Guinea don taimaka musu ta yadda za su tunkari cutar Ebola.

Matakin da gwamnatin kasar Sin ta dauka yana daya daga cikin shirin taimako zagaye na uku da gwamnatin kasar Sin ta samar wajen yaki da cutar Ebola, da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar a ran 18 ga watan Satumba, kuma yana daga cikin amsa kiran da hukumar WHO ta yi wa kasashen duniya wajen ba da taimako ga kasashen Afirka da abin ya shafa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China