Wata sanarwa da ma'aikatar ta bayar ta bayyana cewa, kasar Sin za ta samar wa hukumar ta WFP dala miliyan 6 wadanda za a yi amfani da su wajen saye da kuma aika abinci zuwa kasashen Saliyo, Guinea da kuma Liberia.
Wannan wani bangare cikin kashe na uku na tallafin da gwamnatin Sin ke bayarwa don yaki da Ebola kamar yadda shugaba Xi Jinping ya sanar a ranar 18 ga watan Satumba.
A cewar hukumar ta WFP kimanin mutane miliyan 1 ne za su yi fama da matsalar abinci a cikin watanni masu zuwa a wadannan kasashen guda uku sakamakon cutar ta Ebola. (Ibrahim)