Bangarorin biyu sun nuna gamsuwa sosai kan mu'ammalar da ake yi tsakanin wasu hukumomin nazarin cututtuka nasu, musamman ma cibiyar yin rigakafi da shawo kan cututtuka ta kasar Sin da cibiyar nazari ta Pasteur ta Faransa, da kwalejin nazarin lafiyar jiki na Faransa da asusun Merieux, ban da haka kuma, suna farin ciki sosai domin ganin yarjejeniyar hadin gwiwa da cibiyar sa ido kan lafiyar jiki ta Faransa da cibiyar yin rigakafi da shawo kan cututtuka ta kasar Sin za su daddale, inda bangarorin biyu sun yi alkawarin cewa, za su hada kai wajen yin nazari da shawo kan kwayoyin cuta ta yin amfani da dakin nazari na P4 dake birnin Lyon na Faransa da dakin nazari na P4 da ake kokarin kafawa a birnin Wuhan na kasar Sin, har ma da kara hadin gwiwa a wurare da ke fama da cutar ta Ebola ta fuskar aikin jin kai da yin musanyar fasahohi tsakanin rukunnonin ba da jiyya, ban da haka kuma, kasashen biyu za su yi kokarin hadin kai da wasu kasashe dake yammacin Afrika da cutar ta fi kamari, domin baiwa musu taimakon inganta tsarin kiwon lafiya. (Amina)