Li Bin ta bayyana haka ne a yayin da take halartar babban taron kiwon lafiya da tsaro na kasa da kasa da aka yi a fadar White House dake birnin Washington ta kasar Amurka.
Yayin da take ba da jawabi, madam Li ta kuma bayyana cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasashen da abin ya shafa, don taimaka wa kasashen Afirka wajen kyautata tsarinsu na yin rigakafi da hana yaduwar cututuka da kuma fuskantar ayyukan gaggawa, ta yadda za a iya taimaka musu wajen kafa tsarin kiwon lafiya da tsaro yadda ya kamata. Haka kuma, kasar Sin tana son nuna goyon baya ga taron bisa fannoni daban daban da abin ya shafa, da kuma yin musayar ra'ayoyi kan fasahohin yin rigakafi da hana yaduwar cututuka.
Bugu da kari, a yayin taron, Li Bin ta yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su dauki matakai yadda ya kamata don ba da taimakon gaggawa ga kasashen dake fama da cutar Ebola, da kuma nuna goyon baya ga jama'ar dake kasashen. (Maryam)