Daga ranar 8 zuwa 9 ga watan nan da muke ciki, a madadin gwamnatocin kasashen Sin da Saliyo ne jakadan kasar Sin dake kasar Saliyo Zhao Yanbo, da ministan kula da harkokin diplomasiya da hada kai da kasashen ketare na kasar Saliyo Samura Kamara, suka sa hannu kan wata yarjejeniya game da samar da tallafi ga Saliyo da kasar Sin za ta yi.
An ce, tallafin na wannan karo wani sashi ne na ayyukan da kasar Sin ke gudanarwa domin taimakawa kasar Saliyo wajen tinkarar yaduwar cutar Ebola. Hukumar shirin samar da abinci da aikin gona ta MDD (WFP) ce za ta dauki nauyin sayen kayan abincin, da kuma jigilar su zuwa Saliyo, domin taimakawa jama'ar kasar dake fama da cutar Ebola. (Bilkisu)