in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya yi kira ga hadin gwiwar kasa da kasa domin yaki da Ebola
2014-10-22 11:06:21 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi hira ta wayar tarho a ranar Talata tare da babban sakatare na MDD Ban Ki-moon kan barazanar cutar Ebola dake karuwa, tare kuma da yin kira ga gamayyar kasa da kasa wajen yin aiki hannu da hannu domin yaki da cutar Ebola. Li Keqiang ya jaddada cewa, Sin da Afrika, dukkansu kasashe ne masu tasowa, kuma suna samun alfanu bisa ga dadadar huldar abokantaka, mista Li ya tabbatar da cewa, bangaren kasar Sin na nuna damuwa sosai kan halin da ake ciki a kasashen dake fama da Ebola. Haka kuma ya tunatar da cewa, Sin ta tura taimakon jin kai na gaggawa tun bayan bullowar wannan annoba, kuma tun wannan lokacin ta aika taimakon gaggawa sau da dama, tare da tura adadi da yawa na kwararru da ma'aikatan lafiya a cikin yankunan da cutar ta fi kamari domin taimakawa ga kokarin yin rigakafi da sanya ido. Yanzu kasar Sin na shirin aike da wani sabon taimako da ya hada da karfafa taimakon kiwon lafiyar jama'a, bisa burin taimakawa kasashen Afrika kara kyautata karfinsu na yin rigakafi da sanya ido kan cututtuka, in ji mista Li.

Kasar Sin tana nuna muhimmaci sosai kan gidauniyar da MDD ta kafa, kuma za ta samar da nata taimako bisa gwargwadon karfinta, in ji mista Li tare da cewa, kasar Sin ta nuna yarda da MDD ta rike babban matsayinta na tafiyar da aiki da kulawa da taimakon da ake baiwa Afrika domin yaki da cutar Ebola.

A nasa bangare, Ban Ki-moon ya sanar da mista Li da kokari da maida hankalin MDD kan wannan matsala, tare da nuna yabo ga taimakon da kasar Sin take baiwa kasashen dake fama da cutar Ebola, da kuma taimakon da take baiwa MDD. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China