Shen Danyang ya bayyana hakan ne a gun taron manema labarai da ma'aikatar ta kasuwanci ta kasar Sin ta kira a wannan rana, inda a cewarsa, gudunmmawar ta shafi kayayyakin agaji da abinci da tsabar kudi da likitoci da kuma dakunan binciken cututtuka masu tafi da gidanka da sauransu.
Shen ya kara da cewa, a halin yanzu, kasar Sin ta kammala samar da gudummar da ta alkawarta a karo na farko da na biyu, a yayinda take kokarin tabbatar da gudummawar da za ta samar a karo na uku.
Shen ya ce, gwamnatin kasar Sin za ta samar da gudummawar da ta iya bisa ga yanayin da ake ciki da kuma bukatun kasashen da abin ya shafa, haka kuma za ta yi kokarin inganta hadin gwiwar kiwon lafiya a tsakanin Sin da Afirka, don taimakawa kasashen Afirka inganta kwarewar tinkarar cututtuka da tsarin kiwon lafiyar al'umma.(Lubabatu)