Jam'iyyar NCP ta kasar Sudan dake rike da shugabacin kasar ta amince da tsayar da shugaba mai ci Omar al-Bashir a matsayin dan takararta a ran 25 ga wata don ya shiga babban zabe da za a yi a watan Afrilu na shekarar badi .
NCP ta yanke wannan shawara ne a babban taron wakilan kasar karo na 4 da aka kammala a ran 25 ga wata, yayin taron kuma, an yanke shawarar shugaba Omar al-Bashir zai cigaba da kasancewa shugaban jam'iyyar.
Omar al-Bashir mai shekaru 70 a duniya ya hau kan karagar mulkin kasar Sudan tun shekarar 1993, wanda kuma tsawon lokacin mulkinsa ya kasance mafi tsawo tun bayan da kasar ta samu 'yancin kai daga shekarar 1956. Babban zaben da za a yi a badi shi ne na karon farko da kasar zata shirya tun bayan ballewar Sudan ta kudu a watan Yuni na shekarar 2011. (Amina)