in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya bukaci a tsagaita bude wuta a Sudan ta Kudu
2014-08-26 15:14:01 cri
Babban magatakardan MDD mista Ban Ki-moon ya bayyana gamsuwarsa ga taron da kungiyar bunkasa gabashin Afirka ta IGAD ta shirya a baya bayan nan, domin tattauna batun rikicin kasar Sudan ta Kudu.

Kaza lika babban magatakardan MDDr ya kalubalanci bangarori 2 na Sudan ta Kudun dake arangama da juna, da su tsagaita bude wuta bisa yarjejeniyar da suka kulla ba tare da bata lokaci ba.

Cikin sanarwar da ya fitar ta hannun kakakinsa mista Ban ya lura da yadda gwamnatin kasar Sudan ta Kudu, da dakaru masu adawa da ita suka cimma sabuwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta a ranar 23 ga watan Janairun bana. Game da hakan mista Ban ya yi kira da a aiwatar da wannan yarjejeniya nan take, tare da cika alkawarin da aka dauka na kafa gwamnatin gambiza ta wucin gadi.

Har wa yau sanarwar ta hakaito mista Ban na yabawa kokarin da shugabannin kungiyar IGAD da manzon musamman na kungiyar, bisa kokarin warware rikicin Sudan ta Kudu cikin ruwan sanyi, yana mai jaddada aniyyar MDD ta baiwa hakan cikakken goyon baya. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China