Sanarwar ta ce, kwamitin sulhu yana damuwa da mai da hankali sosai kan tabarbarewar yanayin tsaro da na siyasa da abkuwar bala'in jin kai a sakamakon rikicin da ya barke a Sudan ta Kudu, kuma ya yi Allah wadai da ayyukan keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta sau da dama, tare da jaddada cewa, ba za a amince da yunkurin shugaban Sudan ta kudu Salva Kiir Mayardit da tsohon mataimakinsa Khaled Mashaal na daidaita rikicin kasar ta hanyar makamai.
Dadin dadawa, sanarwar ta ce, kwamitin sulhu ya yi kira ga shugaba Kiir da mataimakinsa Mashaal da sauran bangarorin kasar da su bi yarjejeniyar tsagaita bude wuta, su yi hakuri su tare da aiwatar gudanar da shawarwarin da aka cimmasulhu a birnin Addis Ababa cikin lumana, domin cika alkawarinsu na kafa hadaddiyar gwamnatin rikon kwarya kafin ranar 10 ga wata. Kuma kwamitin sulhu ya y i kashedin daukar matakai kan wadanda suke kawo illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da tsaron kasar Sudan ta Kudu.(Fatima)