Ma'aikatar ta bayyana a cikin wata sanarwa da aka rabawa wa manema labarai cewa, ta gayyaci jami'in harkokin diflomasiyyar kasar Libya da ke Khartoum don nuna rashin jin dadin ta kan bayanan da kafofin watsa labarai ke yayatawa inda kwamandan sojan Libya ke ikirarin neman taimakon Sudan a game da harkokin cikin gidan Libya.
Ma'aikatar ta nanata matsayin Sudan na rashin goyon bayan kowane bangare na kasar ta Libya, tare da mutunta cikakken halaccin zababbiyar majalisar dokokin kasar wadda yanzu haka ta ke zamanta a Tobruk.
Don haka ta bukaci dukkan bangarorin kasar Libya da su sassanta a kokatin sulhunta al'ummomin kasar tare da kaucewa tashin hankalin da ya wargaza al'ummomin kasar.
Tun da farko kwamandan sojojin kasa na Libya Ashraf El Hasi ya bayyana yayin wata hira da tashar talabijin ta larabci mai suna Sky News cewa, Sudan na kokarin tura wasu motoci dauke da mayakan Yemen zuwa kasar Libya,inda aka gano su a garin El-Kufra da ke kan iyaka.(Ibrahim)