in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi maraba da cimma matsaya kan yin shawarwari tsakanin bangarori na Sudan
2014-09-06 16:15:44 cri
Jiya Jumma'a 5 ga wata, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya ba da sanarwar cewa, ana maraba da cimma matsaya da bangarori daban daban na Sudan suka yi kan yin shawarwari tsakaninsu.

Sanarwar ta ce, Ban Ki-moon ya yi maraba da kiran da bangarori daban daban na Sudan suka bayar na yin shawarwari tsakaninsu daga dukkan fannoni da kuma ci gaban da aka samu a wannan fanni. Kuma ya sa kaimi ga bangarorin da abin ya shafa, musamman ma gwamnatin Sudan, da ta samar da yanayi mai kyau ga yin shawarwari tsakaninsu. Bayan haka, Ban Ki-moon ya jaddada cewa, yin shawarwari cikin fahimtar juna da 'yanci zasu ba da taimako wajen daidaita babbar matsalar samun barkewar matsaloli a kai a kai a kasar, da tabbatar da zaman lafiya a Sudan cikin dogon lokaci.

An kuma labarta cewa, jiya kwamitin share fagen yin shawarwari a Sudan da 'yan adawa da gwamnatin kasar sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya a birnin Addis Abeba, hedkwatar Habasha, inda suka cimma matsaya guda kan yin shawarwari a kasar. Kuma abubuwan dake cikin yarjejeniyar sun hada da daina kawo fargaba kan juna, tabbatar da 'yancin siyasa, da sakin fursunonin siyasa da sauransu.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China